Wednesday, July 31, 2019

Tarihin namarudu

 A kasar Iraqi an haka wani kabari inda aka iske gawar Sarki Namarudu da 

matarsa a cikin kabarin

- An ga wasu gwala-gwalai da lu'ulu'u a cikin kabarin wanda aka yi musu kudi 

kimanin dalar Amurka miliyan talatin da biyar

- Sarki Namarudu dai shine sarkin da ba a taba yin Sarki mai arzikinsa ba a tarihi.

An hako gawar Sarki Namarudu a wani yanki dake kasar Iraqi, gawar ta sa da ta matarsa an same su sanye da kaya na gwala-gwalai da lu'ulu'u wanda aka yi musu kudi kimanin dalar Amurka miliyan talatin biyar ($35m), inda kudin ya kai kimanin naira biliyan sha biyu a kudin Najeriya.

Hotuna: An hako gawar Sarki Namarudu da matarsa a kasar Iraqi, an same su sanye da gwala-gwalai na naira biliyan 12
Sarki Namarudu

Sarki Namarudu dai shine Sarkin da yayi zamani da Annabi Ibrahim (AS), tarihi ya nuna cewa akwai lokacin da Namarudu ya sa bayinsa suka gina wani katon rami ya sanya aka kunna wuta mai karfin tsiya a cikin ramin, sannan ya sanya aka jefa Annabi Ibrahim cikin wutar

Monday, July 29, 2019

WASIYYOYI* *GUDA 5 DAGA* *MANZON ALLAH* *(S.A.W).*

*WASIYYOYI* *GUDA 5 DAGA* *MANZON
ALLAH*
*(S.A.W).*
Manzon Allah (s.a.w) yace: "Waye zai karbi
wadannan Kalmomi
guda 5 daga gareni, yayi Amfani da su, ko ya
Sanar
da wanda zai yi Amfani da su"
Sai Abu Huraira (R.A) yace Ni Zan karba ya
Ma'aikin
Allah.
Sai Manzon Allah (s.a.w) ya rike Hannu na
yace min:-
1. Ka guji Aikata Sabo, Zaka Zamo wanda yafi
kowa Bauta a cikin Mutane.
2. Ka yarda da Abinda Allah Ya baka, Zaka fi
Kowa
Arziki Cikin Mutane.
3. Ka kyautata wa Makobcin ka, Zaka Zamo
(cikakken) Mumini.
4. Ka So Wa Mutane Abinda Kake So Wa
Kanka, Zaka Kasance (cikakken) Musulmi.
5. Kada ka Yawaita Dariya, Domin Yawan
Dariya na
Kashe Zuciya.
"Manzon Allah (S.A.W) Yace Ka Rike su Ko ka
Sanar da Wanda Zaiyi Amfani
Dasu".
Idan ka Tura Wa 'Yan Uwa Musulmai Baka
San Wa Zaiyi
Amfani Dasu Ba, Kaga Ka Samu Ladan
Mutane Masu Tarin
Yawa.
Ubangiji Allah ya bamu ikon aikatawa

https://fairmoney.app.link/referral?referral_code=MS599

https://fairmoney.app.link/referral?referral_code=MS599

Ambaliyar ruwan sama ta mamaye gonaki sama da 300 a jigawa

Ambaliya ruwa ta mamaye gonaki fiye da dari uku a garin Safa dake gundumar Sundumina a karamar hukumar Birnin kudu.
Babban Limamin Safa, Malam Ibrahim Safa ya bayyana haka a lokacin taron gangami da kungiyar taimakon kai-da-kai ta GAKAMAZA ta shirya domin tunkarar ambaliyar.

Ya ce asalin ruwan yana zuwa ne ta hanya daya amma yanzu ruwan ya sake bullo 

da hanyoyin guda shida wadda ya yi ambaliyar cikin gonakin shinkafa da dawa, 

dan haka akwai barazanar abinci a shekara mai zuwa.A nasa jawabin, Mai Unguwar Safa, Malam Usman Bello ya ce sun yi ganuwa guda biyu daga buhuna 

da Hakimin Sundumina ya ba su gudummawa amma sai ruwan ya karya ganawar ya kuma nufi gari.

Mai Unguwar Safa ya yi kira ga Majalisar karamar hukumar Birnin kudu local da 

gwamnatin jiha su kai musu daukin gaggawa tun kafin ambaliyar ta shig cikingari.

A nasa bangaren, shugaban kungiyar taimakon kai-da-kai ta GAKAMAZA, Malam 

.Idi Malam wanda ya yi kira ga jama’ar garin da su ci gaba da kokarin ginawa ruwan ganuwa, ya ce zai sanar da karamar hukumar Birnin kudu halin da ake cik

i domin daukar matakan da suka dace.

Sunday, July 28, 2019

Gwamnatin jigawa ta ce zata raini irin itatuwa wanda sunkai dubu cassa'in

Sashin Raya Gandun Daji na Jihar Jigawa zai raini itatuwan darbejiya da turare da keshiya dubu 90 a bana.

Daraktan Gandun Daji na Jihar, Malam Sunusi Yakubu Babura ne ya bayyana haka a hirar da ya yi da Aminiya, inda ya ce suna rainon itatuwan ne a Hadeja da Ringim inda suke rainon itatuwa dubu 60. Sun kuma raini itatuwan zogale da turare da darbejiya da malaina da sauransu.

Sunusi Babura ya kara da cewa sun rani itatuwan gwaiba da gwandar Masar da sauran itatuwa 2,500, sai dai ya koka game da karancin itatuwan da suka dasa a bana.  Ya ce yanzu haka akwai makarantu da suke bukatar itatuwan, amma babu isassu da za su dasa.

Ya ce, sun ware irin itatuwan da za su raba wa makarantu da asibitoci a jihar da nufin bunkasa lafiyar yara da mata masu juna biyu.

Daraktan ya ce ba za su zuba ido suna kallo wadansu batagari suna lalata dazuzzuka ba, kuma duk wanda suka kama yana satar bishiya ko yanyanke ta zai fuskanci fushin hukumar.

Ya ja hankalin jama’a su guji sare itatuwa ba tare da izinin hukuma ba, inda ya ce yawan sare itatuwan ne kan gaba wajen lalacewar yanayi da kwararowar hamada wadda take barazana tare da lalata gandun daji a jihar.

Iftila'in Ambaliyar Ruwan: An Baiwa Mutane 6000 Agaji

Iftila'in Ambaliyar Ruwan: An Baiwa Mutane 6000 Agaji

Iftila’in Ambaliyar Ruwan: An Baiwa Mutane 6000 Agaji
Iftila’in Ambaliyar Ruwan: An Baiwa Mutane 6000 Agaji

Majalisar kula da abinci ta kasa da hadin gwiwar asusun bada agajin gaggawa da aikin gona sun bada gudummawar kayayyakin agaji ga mutane dubu shida da suka gamu da iftila’in ambaliyar ruwa a yankin Karamar Hukumar Kafin Hausa.

An baiwa kowane mutum kilo giram arba’in na ingantattun iri da injin feshin maganin kwari.

Jami’in kula da bada gudummawar Mista Oluruwaju Kazir ya shawarci wadanda suka samu tallafin da su guji sayar da kayyakin da aka basu, a maimakon haka su yi cikakken amfani dasu wajen bunkasa aikin gona.

Mista Oloruwaju Kazir ya kuma baiwa wadanda abin ya shafa tabbacin basu ingantattun irin shinkafa da masara buhu tara kowannan su nan bada jimawa ba.

Daya daga cikin wadanda suka amfana da tallafin ya yabawa wadanda suka bada gudummawar da gwamnatin jihar jigawa bisa wannan karamci tare da bada tabbacin yin cikakken amfani da kayayyakin ta hanyar da ta dace

Saturday, July 27, 2019

YANDA ZAKA SAMU KUDI A INTERNET

Jama’a barkanku da war haka da fatan kowa yana cikin koshin lafiya.
Sanin kowa ne dai a halin yanzu kusan ko wane daya daga cikin matasa ukku yana mu’amala da kafar sadarwa ta Internet. Mafi yawancin wadannan matasan suna bata kusan dukkan lokacinsu ne wajen yin chatting, karanta labaran kwallo da dai sauransu. Wannan shine abin da ya shagaltar da mutanenmu har ma ya sanya basu kula da wasu manyan damammaki ba da zasu iya amfani dasu domin samawa kansu wasu ‘yan kudade. Wani abin mamaki ma shine kusan ko wane matashi sai ya yo wani aiki sana ya iya samun kudin da zaya iya sayen Data da shi, amma kuma bai san ta yaya shi zaya iya samin kudin a saman Internet din ba. A yau cikin wannan kasida, zamu kawo muku wadansu hanyoyin guda hudu da zaku iya bi domin neman na kashewa a saman Internet.
Da yawa daga cikin mutanenmu suna tunanin cewa sai idan kana da website ne kadai zaka iya samin kudi a saman Internet. Sam wannan labari ba haka yake ba, ku biyo mu domin ganin yadda zaku iya samin kudin ba tare da ka mallaki website ba.
1. ADVERTISEMENT (Talla)
Duk wani wanda ya shahara da shiga Facebook zaya iya baka labarin yanda zaka ga wasu mutane sukan leka daga wannan zaure zuwa wancan, ba kuma komai ke kai su ba sai dai kawai suyi comment da wani link da zasu ce ka shiga domin samin wani abu. Wadannan mutane ba komai suke yi ba face yima wasu kamfanoni talla. Da zaran ka danna wannan adireshin da suka baka to zaka shiga a website din kamfanin da suke yi ma tallar, su kuma za’a basu wani dan kaso na kudi sanadiyyar tura ka da suka yi zuwa wannan shafin. Duk da cewa wadannan mutane suna yin talla ne ta hanyar da mutane ba kasafaye suka cika kulawa ba, kai idan kaso zaka iya yinta ta hanyar da ya kamata. Misali zaka iya sanar da abokanka da kuke chatting da su cewa ga wani abu nan na karuwa shima ya shiga domin ya karu, da zaran ya shiga shima yayi rajista shi kenan kaima zaka sami kasonka.
Akwai kamfanoni da yawa kamar na Online Shopping, kamfanonin layin waya, sauran kamfanoni da suke sayar da kayan masarufi, suna bukatar ‘yan talla a ido rufe saman Internet. To don mi, a mai-makon kai ta bata lokaci kawai wajen chatting, ba zaka amfana da wannan dama ba?
2. AFFILIATE MARKETING (Tallata kayan kamfani/website)
Akwai kuma kamfanonin da zaka yi rajista da su, kamar su QSERVERS , Konga , Jumia, EntireWeb da sauransu. Idan kayi rajista da wadannan kamfanonin zasu baka wani adireshi wanda zaka rika baiwa mutane domin yi musu jagora ya zuwa website din wannan kamfanin. Wasu kamfunnan suna biya ne take da mutum ya ziyarci website dinsu ta hayar wannan adireshi da suka baka, wasu kamfunnan kuma suna jira ne har sai wannan mutum yayi sayayya a wannan kamfanin sana su baka wani kaso daga cikin kudin da ya kashe a wajen sayayyar da yayi.
A mai-makon kai ta bata lokaci wajen yin group chat a whatsapp zaka iya amfani da wannan damar domin tallata wa abokan chatting dinka hajar da wannan kamfanin yake sayarwa ta hanyar sanya adireshin da suka baka a cikin group din.
3. REFERRAL (Jagora)
Referral ko kuma jagora wata hanyace da ake samin kudi da ita ta hanyar jawo wani yazo shima yayi rajista da wannan website din bayan kaima kayi. Mafi yawa, sabbin website da ke bukatar mabiya sun fi bada wannan damar. Bayan haka kuma akwai kamfanonin da ke bukatar masu talla (affilliate) to suma sukan baiwa wadanda suka yi rajista da su wata dama akan suma zasu iya gayyato wadansu mutane su zo suyi musu talla. Duk wanda yayi rajista da wannan kamfani ta hanyar adireshin da suka baka to kaima zaka sami wasu ‘yan kudi. Yawan mutanen da ka jawo yawan kudin da zaka iya samu. Kamfanonin da ke samar da wannan dama sun hada da Konga.com , Jumia,
EntireWeb , Renkutten dadai sauransu.
4. FREELANCE (Kwadago)
Wani sabon salo da kafar sadarwa ta yanar gizo ta dauka shine yadda zaka iya yin aiki a biyaka a saman internet! Kwarai ko Aiki! Wannan wani sabon abu ne wanda ba kowa ya san da shi ba, kuma mutane na samun kudi sosai ta wannan hanya. Kusan duk wata kwarewa da ka sani kana da ita akwai masu bukatar irin wannan. Idan kana da saurin typing, akwai kamfonin da ke yin hayar mutane domin suyi musu typing, idan kana bukatar yin irin wannan aiki zaka searching din “Typing Jobs” a google. Ayyukan da zaka iya samu wannan fage sun hada da
Yin fassara daga wani yare zuwa wani
Koyarwa (Teaching)
Yima wasu Assignment na makaranta
Graphics design
da sauranasu.
Kaga ke nan dan uwa da ‘yar uwa bai kamata ku rika bata lokutanku ba kawai a saman Internet ba tare da kuma kun samu wata hanyar da zaka iya amfana daga hakan.

MATAKAN DA ZAKA FARA BI DOMIN SAMUN KUDI A INTERNET

A wannan lokaci da muke ciki, kafar Internet ta zame ma wasu mutane wata babbar masa’anta inda suke samun kudi ta hanyoyi daban-daban da ke a wannan dandali na internet. Akwai mutanen da wannnan hanyar itace hanya daya tal da suka dogara a kanta domin samun kudi, kuma abin burgewa shine, sai ka ga irin wadannan mutanen suna samu kudin da wasu ma’aikatan ma basa iya samu a wani dan lokaci.
Ganin irin samayyar da ake yi a wannan hanyar ya sanya da dama da mutanenmu sun shiga wannan fage domin suma a dama da su. Sai dai wata matsala da ke tattare da wadannan mutane shine, rashin sanin dami-dami suke bukata kafin su fara shiga wannan harka ta neman kudi a dandalin internet. Wata tambaya da mafi yawan masu bukatar shiga wannan harkar suke yi shine ta wace kafa zasu iya karbar kudinsu idan sun samu? Wannan itace tambayar da muka amsa muku a cikin wannan kasida.
Kafin ka iya karbar kudinka da ka samu a shafin internet, dole ka mallaki Bank account, Debit Card da kuma
online payment account. Ga bayanan wadannan abubuwa da muka fada muku:
Bank Account shine asusun ajiya da zaka bude a wani baneki na gida inda zaka iya zuwa da kanka ka bude wannan account din, kuma ya zamto banki ne sananne kuma babban banki.
Online payment account shine account din da zaka bude a saman Internet wanda da shine za’a iya yo maka transfer na kudin da ka samu. Website na online payment suna da da yawa, amma wanda aka fi amfani da shi shine PayPal. Zaka iya shiga paypal.com domin bude naka account din.
Debit card shine katin katin da zaka iya amfani da shine wajen cire kudi tare da yin wata harka da shafi saye da siyarwa a saman internet. Shi wannan kati, da aka fi sani da suna ATM card, shine zaka yi amfani da shi domin hada Bank Account naka da kuma Online payment account naka ta yanda idan an turo maka kudi zasu biyo ta wannan account sais u shigo a Bank Account naka. Card din da aka fi amfani da su sune da kuma MasterCard Visa. Ka tabbatar bankin da zaka bude account da sha yana bada irin wadannan cards din.
Wadannan sune abubuwa 3 da ya zama dole ka mallaka idan kana bukatar shiga wannan katafaren fage na neman kudi a saman Internet.
Idan har kuna amfanuwa daga kasidojin da SADARWA ke kawo muku, to ku bamu goyon baya tare da karfafa mana guiwa akan abin da muke yi ta zabar SADARWA a matsayin Cibiyar samar da ilimin fasahar sadarwa.
Ka kada kuri'arku sai ku shiga a wannan website din, ku dubo inda aka sanya “Best I.T startup of the year” sai ku taba wajen. Zaku ga wasu jerin sunaye, sai ku zabi
SADARWA , sai kuje daga kasa ku yi Submit.
Da fatan zaku kara mana kwaringuiwa ta hanyar zabarmu a matsayin Cibiyar da ke samarda ilimin fasahar sadarwa.
Ga adress din inda Zaku kafa kuri'ar:

Friday, July 26, 2019

Yanda zaka karbi sakon kiran da akaima lokacin da wayar take kashe

Assalamu’alaikum
warahmatullahi wa barakatuhu
Wannan wata damace da zata
baka damar sanin wanda ya
kiraka alayinka na MTN alokacin
da wayarka take akashe koma
ka cire sim card dinka ka ajiye.
To da zarar ka kunna wayar,
mtn zasu aiko maka da sakon
text message dauke da lambar
wayar wanda ya kiraka bai
sameka dinba alokacin da
wayar taka take akashe/layin
naka yake akasa.
Domin shiga tsarin, yanzu aika
sakon SET 01 Zuwa ga 100.
Nan take zasu aiko maka da
sako kamar haka: Y’ello!
803xxxxxxx request to activate
Who Called with Notify Me
service was successful. Thank
you.
Idan kanaso kagane ko layinka
na mtn yana kan wannan tsarin,
to saika aika da sakon STATUS
Zuwa ga 100.
YADDA ZAKA CIRE LAYINKA NA
MTN DAGA TSARIN…
Domin fita daga tsarin, saika
aika da wadannan kalmomin
DELETE Zuwa ga 100.
Zasu aiko maka da sako kamar
haka: Y’ello! 803xxxxxxx
request to deactivate Who Called
service was successful. Thank
you
Wannan yana aiki akan duk
tsarukan da mtn suke dashi,
kuma kyautane.

YADDA ZUKU KULLE KUDIN CIKIN LAYIKAN WAYARKU

Assalamu’alaikum
warahmatullahi wa barakatuhu
Kuyi amfani da wadan nan
lambobin *33#0000# domin
rife kudin da suke a acount
dinku
wadannan lambobi suna
taimakawa ta yadda wani ba zai
yima amfani da kudin layinka
ba, har sai idan kaine ka bude
account din naka da kanka.
Idan ka tashi budewa to saika
danna wadannan lambobin
kuma #33*0000# saiku tura
kira
accoun din zai bude sai aci
gaba da yin kira!
MAHIMIYAR SANARWA!
Wadannan lambobi basa aiki
akan layin mtan
Wassalamu’alaikum
warahmatullah

YADDA ZAKA KARE A CCOUNT DINKA NA FACEBOOK DAGA MACUTAN YANAR GIZO

Assalamu’alaikum
warahmatullahi wa barakatuhu
Mahimin abu wanda galibin
mutanen da keyin facebook
basu san da shiba shine yadda
zasu kare facebook dinsu daga
mutanen da suka kware wajan
kwatarwa mutane account a
facebook
Wasu kuma sun sani amma
saboda hatsarin hanyar yasa
sukayi watsi da ita.
Wasu kuma tuni suka dade da
bin wannan hanyar domin
ganin sun ba account dinsu
kariya.
HANYOYIN BADA KARIYA GA
FACEBOOK SUNKAI KAMAR KASHI
3.
1. Hanya mafi tsauri itace wacce
zakai amfani da wasu code
wadanda facebook zasu baka,
Matsalarta itace idan ka manta
wadannan code din to account
dinka ya tashi aiki, saboda aduk
lokacin da zakayi login sai sun
tambayeka wannan scurity code
din da suka baka.
2. Zaka zabi kalar browser da
kake aiki da ita kasa musu, sai
su baka wasu code wadanda
aduk lokacin da za’ai login din
account dinka da wata browser
nanma sai ansa wannan code
din sannan account din zai
bude.
3. Wannan itace hanya mafi
sauqi kuma mafi akasari
mutane yanzu ita suke bi domin
bada kariya a ccount dinsu na
facebook
dan haka nima yanzu akanta
zan maku bayani.
YADDA HANYAR TAKE KUWA
SHINE…
Idan kana amfani da ita to duk
lokacin da wani yake kokarin
hawa maka account batareda
umarninka ba to facebook
zasuyi gagawar sanar da kai ta
hanyar sakon text message
zuwa lambar wayarka
dan haka da zarar sun sanar da
kai to wani yana kokarin
hawama account saika maza ka
hau ka dauki matakin canja
password.
YADDA ZAKA CANJA PASSWORD
br /> Ka hau facebook dinka ka
tafi can kasa, ka shiga inda kaga
an rubuta setting & privacy
bayan yabude saika shiga
General, bayan ya bude saika
zabi password kashiga, idan
yabude zasu umarceka dakasa
password dinka a box din
farko, a box na biyu saikasa
sabon password din daka ke
son canjawa, a box na ukuma
kasa sabon, sannan kadanyi
kasa kadan zakaga change
saika shiga, to da zarar ka canja
kaga ka gama da wancen mai
kokarin hawama account.
YADDA ZA’A SAKA WANNAN
TSARIN br />
Idan ka hau facebook dinka
saika tafi zuwa can kasa ka
shiga inda kaga an rubuta
Settings &Privacy
idan ya bude saika zabi security
ka shiga, da ya bude saika zabi
‘Text Message Login
Notifications da E-mail
Login Notification.
zakaga daga gabansu kadan
akwai blue din rubutu ansa
‘Desable to saika hau kanshi
kayi ok! da yagama Loading
zakaga ya koma ‘Enable Amma a
Text Message Login
Notifications, saika sake
comfirm na password dinka
shikenan daga nan kaga ma
Kuma ko waye zaiyi login din
account dinka sai ansanar da
kai ta Lambar wayarka, koda
kuwa kaine kayi login din da
wata sabuwar browser
matukar layin da ka bude
facebook yana akan wayarka to
sai sun sanar da kai ko ta email

YADDA AKE JUYAR DA KIRAN DA BA’A SON SHIGOWAR SHI

YADDA AKE JUYAR DA
KIRAN DA BA’A SON
SHIGOWAR SHI
Assalamu’alaikum
warahmatullahi wa barakatuhu
Yadda ake juyar da kiran da
ba’a son shigowarsa
kamar masu damunka da
flashing
Sau da dama wasu mutane
sukan dameka da kira ba gaira
babu dalili,. alhalin bawani abu
zasu fadamaka muhimmiba
idan wan nance matsalarka sai
ince daga yau kayi bankwana
da ita.
Kawai abinda zakayi shine ka
danna*257*1# dan juyar
dakowane irin kiran da zai
shigo.
Idan kuma kanaso ka cire saika
danna*257*2#.
Idan kuma sokake ka sa lambar
mutum shika dai a blacklist
wato wadanda in sun kira
bazasu same kaba, to sai kawai
ka danna *257*4*lambar
mutumin# saika danna send.
Idan kuma kana so ka cireshi
daga black listdin saika
danna*257*5*lambar
mutumin#
shikenan ka cireshi.
Wassalamu’alaikum
warahmatullah.

Dariya zallah su malam an sha miyar tausje

Dariya Zallah: Su Malam An Sha Miyar Taushe
Dariya Zallah: Su Malam An Sha Miyar Taushe

Wani Malami yaje gidan wani attajiri sai aka kawo masa tuwon shinkafa miyar taushe da naman kaji me yawa, malam yaci tuwo da naman kaji yayi dam.

Sai yace Allah ka kara tsira da aminci ga annabi Shu’aibu: sai me gidan yace toh Allah gafarta malam wani abu ne ya faru? Sai malam yace Ehhhh “Ai shine yayi addu’a kaji suka daina tashi sama

Thursday, July 25, 2019

Amfanin gwaza a jikin dan a dam

Amfani Gwaza Da Ganyensa A Jikin Dan Adam
Amfani Gwaza Da Ganyensa A Jikin Dan Adam

Binciken da kwararru suka yi game da ganyen gwaza sun gano cewa yana dauke da sinadarai masu yawa wanda ke kawar da cututtuka kamar su hawan jini, cutar daji, makanta da sauransu.

Kwararrun sun yi kira ga mutane da su riƙa yawaita cin gwaza da cewa yana da matuƙar amfani a jikin mutum.

Za a iya samun wannan amfanin ne idan aka dafa gwaza ko kuma ganyen a matsayin abinci ko kuma a yi miya da shi.

A arewacin Nijeriya kuwa akan dafa gwaza domin a ci shi haka nan, ko da manja ko man gyada ko kuma miya.

1. Ganyen gwaza na dauke da sinadarin ‘Vitamin C’ wanda ke kare mutum daga kamuwa da cututtuka.

2. Yana kare mutum daga kamuwa da cutar daji ta kowace iri.

3. Yana ragewa da kare mutum daga kamuwa da cutar siga ‘Diabetes’.

4. Ganyen gwaza na dauke da sinadarin ‘Vitamin A’ wanda ke kara karfin ido sannan da kare ido daga kamuwa da cututtuka kamar su yanar ido,amosanin ido, makanta da sauran su.

4. Yana taimakawa wajen nika abinci, kawar da ciwon ciki sannan da hana yawan yin bahaya.

6. Yana hana fatar mutum tsufa da sauri sannan da kawar da cututtukan dake kama fata.

7. Yana ƙara ƙarfin jijiyoyin jiki

8. Ganyen walaha na kere mutum daga kamuwa da hawan jini

9. Yana dauke da sinadarin ‘Calcium’ wanda ke kara karfin ƙashi.

10. Ganyen walaha na dauke da sinadarin ‘Folate’ wanda ke inganta girman dan dake ciki sannan da hana mace mai ciki kamuwa da hawan jini

11. Yana kara jini a jiki musamman ga yara kananan.

12. Kara kaifin kwakwalwar mutum musamman wajen hana mantuwa.

13. Yana inganta maniyi a jikin maza.

Wednesday, July 24, 2019

Turkashi:ma'aikatan gidan tsohon shugaban kasar Nigeria Goodlock joanatan sun saci gwala gwalai na naira miliyan 300

- Wasu masu aikin gidan tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan sun sace masa wasu gwala-gwalai masu tsadar gaske

- An kiyasta kudin gwala-gwalan cewa kudinsu zai kai kimanin naira miliyan dari uku, sannan kuma sun dauki wata sanda da tsohon shugaban kasar yake amfani da ita yana dogarawa

- An bayyana cewa jami'an 'yan sanda dai sun cafke wasu daga cikin wadanda ake zargin ciki kuwa hadda wadanda suke da dangantaka da tsohon shugaban kasar

A halin yanzu dai ana gabatar da wani kwakkwaran bincike akan masu aikin gidan tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan da 'yan uwansa, bayan an nemi gwala-gwalai da kudinsu ya kai kimanin naira miliyan dari uku, wanda suke mallakin tsohon shugaban kasar.

Wata mata da ake zargi da take aiki a gidan shugaban kasar mai suna, Mrs. Jonathan Aridolf Resort, ana zargin ta samo irin mukullin dakin da gwala-gwalan suke ajiye a ciki.

Jaridar The Nation ta bayar da rahoton cewa wacce ake zwrgin ta shiga gidan shugaban kasar dake Otuoke, cikin karamar hukumar Ogbia, ta dauki gwala-gwalan ciki hadda wata sandarshi ta dogarawa.

"Ba bako ne yayi wannan aikin ba. Barawon ya riga ya san gidan nan. Sun yi niyyar ha'inci ne. Daya daga cikinsu mai aikine, wanda ke rike da mukullin dakin da gwala-gwalan ke ajiye a ciki.

"Sauran kuma suna da dangantaka da tsohon shugaban kasar. Na san jami'an 'yan sanda sun kama wasu daga cikinsu. Ba zan iya fadar kudinsu ba, matar tsohon shugaban kasar ce kawai za ta iya fadar kudinsu.

"Sun riga sun bayyana cewa su suka yi, har an samu an karbi kudin daga hannun wasu daga cikinsu," in ji wani wanda lamarin ya faru a gabansa.

Daga baya an bayyana cewa matar tsohon shugaban kasar Patience Jonathan ta shiga rudani akan satar, inda take mamakin yadda aka yi wadanda ake zargin basu saci gwala-gwalan nata ba suka saci na mijinta.

YADDA ZAKA BUDE WEBSITE NAKA CIKIN SAUKI

Da website ne ake yada labarai, wa'azozi, nasihohi, kasuwanci, tarihi, kide kide da wake wake. Shi website ba sako ake karɓa ko aikawa dashi ba kamar Email, a'a shi zaka yi rubutu ne kamar yadda kake yin post a Facebook. Rubutun zai zauna har abada duk wanda ya shiga website dinka ko daga wane bangare na duniya ne, zai gani matukar ba kaine ka goge rubutun ba.
Haka nan duk wanda yayi searching wani abu a Google ko Bing ko Ask, idan dai abinda yake nema yana da alaka da daya daga cikin rubutun ka, to Google zasu yi mashi ishara da website dinka cikin jerin websites din da zasu turo mashi. Wannan kuwa ba lallai bane ka sani Good yayi maka wannan kokarin ba.
MISALIN WEBSITE DIN DA ZAKA IYA KIRKIRA
1- Website na labarai kamar www.bbchausa.com
2- Website na technology kamar namu wato www.sirrinwayarandroid.blogspot.com.ng
3- Website na kade kade da wake wake kamar www.mawakanhausa.org
4- Website na videos kamar www.hausamedia.ml
5- Website na nasihohi da wa'azozi kamar www.darulfikr.com da dai sauran su.
YADDA ZAKA FARA
Na zabi hanya mafi sauki don ba ma kowa damar iya mallakar shafi nasa na kansa. Don haka zamu dauki na kamfani Google ne don shi ne mafi sauki.
ABUBUWAN DA AKE BUKATA
1- Gmail
2- Lambar waya
3- Waya mai caji da kuma data
Bayan ka mallaki duk abubuwan da na lissafa a sama to yanzu kusan in ce maka ka gama mai wuyar sai dai karasawa. Ba tare da na cika ka da surutu ba,
danna nan don yin register.
Da zaran ka shiga zai nuna maka wani page da zaka ga create your blog Sai kayi clicking akan sa.
Zai kai ka wani page da zai tambaye ka Gmail dinka sai ka sanya Email da password dinka
LURA
Duk wani Email da zaka sanya wanda ba Gmail ba to ba zai yi ba don su Google basa amfani da duk wani Email wanda ba nasu ba.
Bayan ka cike wannan next page da zaka gani shi ne wani page wanda zasu nuna maka Email dinka da kuma phone number dinka, to anan sai kayi kasa zaka ga wani Bulan rubutu an rubuta "DONE"sai kayi clicking dinsa.
Daga nan zai kai ka wurin da zaka rubuta page title da kuma page address naka. Page title shine wani rubutu da zaka gani daga saman shafin farko na kowane website. misali kana iya sanya BARKA DA ZUWA ko kuma
SHAFIN WAYAR DA KAN MATASA. ko dai duk abinda kake bukata.
A bangare daya kuma page address shine sunan website dinka wanda duk wanda ya rubuta shi a browser dinsa to automatically zata kai shi shafin ka ne. To anan ka tabbatar ka zabi sunan da kake da tabbacin babu wanda yake da irin sa. Don ba'a website iri daya guda biyu, duk wanda ka gani shi kadai ne duk duniyar nan.
Duk abinda ka rubuta zai zama kamar haka www.misali.blogspot.com wato a inda na sanya misali to sunan da ka sanya shi ne zai maye gurbin sa.
Bayan ka kammala wannan page din to yanzu fa ka mallaki website naka na kanka abinda ya rage maka content wato abinda website din naka zai kunsa.
Daga nan zai kai ka dashboard naka wato wurin da zaka rika controlling website din naka. Zaka ga page title dinka daga sama. Sai ka duba hannun hagun screen dinka zaka ga NEW POST. Sai kayi clicking dinsa zai nuno maka wani page mai column biyu na farko zaka ga an rubuta post title to shine heading na post dinka. Kamar yadda kaga mun sanya YADDA ZAKA KIRKIRI WEBSITE NAKA.
Sai ka shiga column na biyu nan zaka rubuta duk labarin ka sai kayi clicking akan publish. Da zaran ka yi clicking publish to fa yanzu kayi nasarar posting din rubutun ka na farko.
Don jarrabawa sai ka ba wani abokin ka ko kayi amfani da wata wayar ka shiga website din naka don gane ma idon ka abinda ka rubuta da kuma yadda ya fito.

Yadda zaka samu kudi ta hanyar bude dandali a yanar gizo By Bashir masanawa

Harkar samun kudi a yanar gizo na da yawan gaske a wannan lokaci kuma akwai riba, amma fa sai anyi da gaske. Za’a iya yin shafi a wasu dandalin kamar na facebook, amma a tuna cewa duk karin mutanan da kayi a shafin facebook, kana karawa facebook suna, da kuma kudi. Mun amince cewa facebook sunyi nisa, amma kowa zai iya amfani dasu wajan yada dandalinsa na yanar gizo don samun alheri.
Idan aka bude dandalin “build your website” wato “gina naka shafin intanet”, za’a iya saka tallace-tallacen abubuwan saye da sayarwa har wadanda sauran mutane ke tallatawa; tallace-tallace kamar na google adsence, Yahoo, Microsoft da-dai sauransu duk ana iya sakawa.
Hanyar samun kudi ta tallata manhaja, wato “advertisement”:
Wannan hanyar tafi kowace hanya sauki ta fannin samun kudi ta shafin yanar gizo, kuma duk duniya amfi amfani da ita. Idan kana/kina da dandali dayake da abubuwa masu ma’ana (misalin kamar shafin wannan shafin “Bimas computer”) kuma mutane na zuwa dandalin za’a iya sa tallar “adsence” idan akayi rijista da “google adsence”. Abun da kawai ake bukata shine asusun banki da dalar Amurka, wato “domiciliary account” da kuma adireshin meshafi da google din zasu aikoma mutum da check idan ya/ta sami riba. Check din a dalar Amurka yake zuwa, to dolene a tanadi asusun. Zai fidacewa idan mutum ya hada da adireshin “post office” wato P.O.Box wajan adireshin tura sakonni a google.
Idan akasa talla daya, google nabiya a duk sanda wani me ziyartar shafin ka/ki ya danna shafin tallar. Ba wani kudi dayawa ake samuba, amma ana iya samun kudinda suka kai N1.00 har zuwa dun=baunnai masu yawa. Kar a manta, sai ana da shafi mai ma’ana sannan za’a samu mutane su zo dandalin.
Hanyar samun kudi ta hadayyar dandali wato “Affiliate programs”:
A wannan hanyar kuma, zaka sa hanyar hadayya (link) zuwa wasu dandalin kamarsu “Amazon” (wato shafuka na cinikayya da saye da sayarwa) idan akayi rijista da affiliate program dinsu wanda rijistar anayine a shafin nasu. Idan wanda yaje dandalinsu ta dandalinka yayi siyayya, to zasu baka kashin ribar batare da kayi komaiba.
Hanyar samun kudi ta dandalin siye da siyarwa wato “Ecommerce”:
Wannan hanyar tafi dacewa da harkar me shago, ko mai siye da siyarwa. Ma’ana, idan sana’ar mutum itace ya saya ya siyar to wannan hanyar zatafi dacewa da shi/ita. Zaka/zaki bude dandalin ka/ki, a saka hotunan kayan siyarwar da kuma wasu karin bayanai kamar lambar waya inda idan mutun yaga hotunan kayan yana sha’awar siye zai iya siyayyarsa ta dandalin. misali irin wannan dandali shine Jumia.
Idan mutun bashi da halin bude nasa dandalin a yanar gizo, to zai iyam amfani da wanda muke da shi akan wanna dandalin. Jeka sashen Kasuwa/Classified ads
Idan da neman karin bayani akan yadda za’a iya bude dandali a yanar gizo, to a tuntubemu a Bimas computer
Dan Karin bayani, sai ayi comment a nan kasa. Dafatan anyi rijista da mu.
Allah yabamu sa’a gaba daya
Karin bayani.
Atakaice abunda muke fada anan shine: zaka iya bude website dinka, ka saka tallunan google, da wasu companinnikan dan ka samu kudi. Sannan idan kanaso ka jawo mutane zuwa website dinka, zaka iya amfani da da facebook wajan jawo mutanen. Idan mutanen sukazo shafin naka suka danna (click) akan tallar, zaka samu yan chanji duk sanda aka danna tallar. Nan bada dadewaba, zamuyi sharfin yadda zaka iya bude website dinka ta hanya mafi sauki. Mungode

Kun san matan da ke cikin sabbin ministocin Buhari?

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya aika sunayen mutum 43 a matsayin ministocinsa ga Majalisar Dattajai don tantancewa a ranar Laraba.
Mata bakwai ne kacal suka samu shiga jerin.
A yayin da wasu mutanen ke yabonsa kan yawan matan da ke jerin, wasu kuwa suka suke kan cewa yawan ya ragu.
Ko su waye wadannan mata?
Wadannan mata dai da suka shiga jerin ministoci gogaggu ne a fannoni daban-daban kamar bangaren harkar kudi da gwamnati da ma Majalisar Dinkin Duniya.
Sannan kuma masu ilimi ne a fannoni daban-daban.
Zainab Ahmed - (Kaduna)
Zainab Ahmed ce tsohuwar ministar kudi a karo na farko na mulkin Shugaba Buhari na 2015, inda aka nada ta a watan Satumbar 2018 bayan da Kemi Adeosun ta yi murabus.
Zainab tana da digiri a karatun Akanta da digiri na biyu a Gudanar da Harkar Kasuwanci.
A shafinta na Twitter an rubuta cewa tana da kwarewa a fanin mu'amalar kudi ta tsawon shekara 28.
Sharon Ikeazor - (Anambra)
Sharon Ikeazor ce shugabar hukumar fanshon ma'aikatan gwamnati (PTAD) wacce Shugaba Buhari ya nada ranar 26 ga watan Satumbar 2016.
Rahotanni sun ce a shekararta ta farko a ofis, ta gabatar da tsare-tsare da dama da suka kawo sauyi a hukumar ta PTAD.
Tana da digiri a fannin shari'a daga Jami'ar Benin da kuma takardar shaidar kammala makarantar koyon shari'a a 1985.
A shafinta na Twitter an rubuta cewa tana son ci gaban Najeriya da ganin an bai wa mata damarmaki.
Sadiya Farouq (Zamfara)
Sadiya Farouq ita ce shugabar hukumar 'yan ci-rani da 'yan gudun hijira.
Tana da digiri a Gudanar da Harkar Kasuwanci daga Jami'ar Ahmadu Bello Zaria a jihar Kaduna da kuma digiri na biyu a harkokin kasasehn waje da diflomasiyya duk daga wannan jami'ar.
Ambasada Maryam Yalwaji Katagum (Bauchi)
Maryam Yalwaji Katagum ita ce Jakadiyar dindindin ta Najeriya a UNESCO tun watan Yunin 2009.
Ta yi digirinta na biyu kan sha'anin mulki da tsare-tsare a Jamiar Legas, sai digiri na farko inda ta karanta harshen Turanci, ta samu shaidar kammala karatu a fannin Ilimi daga ABU Zaria da shaidar kammala karatu a University College, London.
Gbemi Saraki (Kwara)
Gbemi Saraki tsohuwar sanata ce da ta wakilci yankin Kwara ta Tsakiya kuma kanwar tsohon shugaban majalisar dattajai Bukola Saraki ce.
Ta yi digirinta na farko a Jami'ar Sussex da ke Birtaniya inda ta karanci Tattalin arziki.
Ramatu Tijani (Kogi)
Ramatu Tijani ita ce tsohuwar shugabar ata ta jam'iyyar APC ta kasa.
A wata hira da ta taba yi da Jaridar Nation a 2018, ta ce ta halarci Jami'ar Ahmadu Bello Zaria inda ta karanci fannin Tsara birane.
Ta yi digiri na biyu a Sha'anin Mulki. A lokacin ta kara da cewa tana karatun digirin digirgir dinta a fannin Tsaro a wannan ABU din.
Pauline Tallen - (Plateau)
Pauline Tallen tsohuwar mataimakiyar gwamnan Jihar Filato ne a 2007 kuma mace ta farko da ta rike wannan mukamin a arewacin Najeriya.
A shekarar 1999 ta zamo Ministar Kimiyya da Fasaha a lokacin tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo. Ta kuma taba yin takarar zama gwamnar Filato a 2011 amma sai Jonah Jang ya kayar da ita.

AN KAIWA JARUMIN FINA FINAI HARI DA WUKA A CHAINA

An kaiwa shahararren jarumin fina-finai dan Hong Kong Simon Yam Tat-wah hari da wuka a yayinda yake gudanar da wasa kan minbari a China.

An kaiwa jarumin fina-finai hari da wuka a China

An kaiwa shahararren jarumin fina-finai dan Hong Kong Simon Yam Tat-wah hari da wuka a yayinda yake gudanar da wasa kan minbari a China.

Hukumar 'yan sandan Congshan dake jihar Guangdong sun bayyana cewar jarumin Yam da aka kaiwa hari da wuka an kwantar dashi a asibiti amma rayuwarsa bata cikin hadari.

An dai kama maharin wanda aka bayyana yana fama da ciwon schizophrenia watau tabin hankali.

Wasu daga cikin matsaloli da yan film me fuskanta a duniya

Wasu daga cikin matsallolin da yan wasan Fim ke fuskanta a Duniya
Anne-Elisabeth Bossé daya daga cikin yar wasar Fim a Duniyar Fina-Finai

A cikin shirin Dandalin fasahar Fina-Finai,Hawa Kabir ta mayar da hankali ga rayuwar yan Fim a Najeriya da wasu kasashe da suka hada da India,musaman labarin da wasu mutane ke bayar na mutuwar yan wasan Fim.