Jama’a barkanku da war haka da fatan kowa yana cikin koshin lafiya.
Sanin kowa ne dai a halin yanzu kusan ko wane daya daga cikin matasa ukku yana mu’amala da kafar sadarwa ta Internet. Mafi yawancin wadannan matasan suna bata kusan dukkan lokacinsu ne wajen yin chatting, karanta labaran kwallo da dai sauransu. Wannan shine abin da ya shagaltar da mutanenmu har ma ya sanya basu kula da wasu manyan damammaki ba da zasu iya amfani dasu domin samawa kansu wasu ‘yan kudade. Wani abin mamaki ma shine kusan ko wane matashi sai ya yo wani aiki sana ya iya samun kudin da zaya iya sayen Data da shi, amma kuma bai san ta yaya shi zaya iya samin kudin a saman Internet din ba. A yau cikin wannan kasida, zamu kawo muku wadansu hanyoyin guda hudu da zaku iya bi domin neman na kashewa a saman Internet.
Da yawa daga cikin mutanenmu suna tunanin cewa sai idan kana da website ne kadai zaka iya samin kudi a saman Internet. Sam wannan labari ba haka yake ba, ku biyo mu domin ganin yadda zaku iya samin kudin ba tare da ka mallaki website ba.
1. ADVERTISEMENT (Talla)
Duk wani wanda ya shahara da shiga Facebook zaya iya baka labarin yanda zaka ga wasu mutane sukan leka daga wannan zaure zuwa wancan, ba kuma komai ke kai su ba sai dai kawai suyi comment da wani link da zasu ce ka shiga domin samin wani abu. Wadannan mutane ba komai suke yi ba face yima wasu kamfanoni talla. Da zaran ka danna wannan adireshin da suka baka to zaka shiga a website din kamfanin da suke yi ma tallar, su kuma za’a basu wani dan kaso na kudi sanadiyyar tura ka da suka yi zuwa wannan shafin. Duk da cewa wadannan mutane suna yin talla ne ta hanyar da mutane ba kasafaye suka cika kulawa ba, kai idan kaso zaka iya yinta ta hanyar da ya kamata. Misali zaka iya sanar da abokanka da kuke chatting da su cewa ga wani abu nan na karuwa shima ya shiga domin ya karu, da zaran ya shiga shima yayi rajista shi kenan kaima zaka sami kasonka.
Akwai kamfanoni da yawa kamar na Online Shopping, kamfanonin layin waya, sauran kamfanoni da suke sayar da kayan masarufi, suna bukatar ‘yan talla a ido rufe saman Internet. To don mi, a mai-makon kai ta bata lokaci kawai wajen chatting, ba zaka amfana da wannan dama ba?
2. AFFILIATE MARKETING (Tallata kayan kamfani/website)
Akwai kuma kamfanonin da zaka yi rajista da su, kamar su QSERVERS , Konga , Jumia, EntireWeb da sauransu. Idan kayi rajista da wadannan kamfanonin zasu baka wani adireshi wanda zaka rika baiwa mutane domin yi musu jagora ya zuwa website din wannan kamfanin. Wasu kamfunnan suna biya ne take da mutum ya ziyarci website dinsu ta hayar wannan adireshi da suka baka, wasu kamfunnan kuma suna jira ne har sai wannan mutum yayi sayayya a wannan kamfanin sana su baka wani kaso daga cikin kudin da ya kashe a wajen sayayyar da yayi.
A mai-makon kai ta bata lokaci wajen yin group chat a whatsapp zaka iya amfani da wannan damar domin tallata wa abokan chatting dinka hajar da wannan kamfanin yake sayarwa ta hanyar sanya adireshin da suka baka a cikin group din.
3. REFERRAL (Jagora)
Referral ko kuma jagora wata hanyace da ake samin kudi da ita ta hanyar jawo wani yazo shima yayi rajista da wannan website din bayan kaima kayi. Mafi yawa, sabbin website da ke bukatar mabiya sun fi bada wannan damar. Bayan haka kuma akwai kamfanonin da ke bukatar masu talla (affilliate) to suma sukan baiwa wadanda suka yi rajista da su wata dama akan suma zasu iya gayyato wadansu mutane su zo suyi musu talla. Duk wanda yayi rajista da wannan kamfani ta hanyar adireshin da suka baka to kaima zaka sami wasu ‘yan kudi. Yawan mutanen da ka jawo yawan kudin da zaka iya samu. Kamfanonin da ke samar da wannan dama sun hada da Konga.com , Jumia,
EntireWeb , Renkutten dadai sauransu.
4. FREELANCE (Kwadago)
Wani sabon salo da kafar sadarwa ta yanar gizo ta dauka shine yadda zaka iya yin aiki a biyaka a saman internet! Kwarai ko Aiki! Wannan wani sabon abu ne wanda ba kowa ya san da shi ba, kuma mutane na samun kudi sosai ta wannan hanya. Kusan duk wata kwarewa da ka sani kana da ita akwai masu bukatar irin wannan. Idan kana da saurin typing, akwai kamfonin da ke yin hayar mutane domin suyi musu typing, idan kana bukatar yin irin wannan aiki zaka searching din “Typing Jobs” a google. Ayyukan da zaka iya samu wannan fage sun hada da
Yin fassara daga wani yare zuwa wani
Koyarwa (Teaching)
Yima wasu Assignment na makaranta
Graphics design
da sauranasu.
Kaga ke nan dan uwa da ‘yar uwa bai kamata ku rika bata lokutanku ba kawai a saman Internet ba tare da kuma kun samu wata hanyar da zaka iya amfana daga hakan.
No comments:
Post a Comment