Wednesday, July 24, 2019

Turkashi:ma'aikatan gidan tsohon shugaban kasar Nigeria Goodlock joanatan sun saci gwala gwalai na naira miliyan 300

- Wasu masu aikin gidan tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan sun sace masa wasu gwala-gwalai masu tsadar gaske

- An kiyasta kudin gwala-gwalan cewa kudinsu zai kai kimanin naira miliyan dari uku, sannan kuma sun dauki wata sanda da tsohon shugaban kasar yake amfani da ita yana dogarawa

- An bayyana cewa jami'an 'yan sanda dai sun cafke wasu daga cikin wadanda ake zargin ciki kuwa hadda wadanda suke da dangantaka da tsohon shugaban kasar

A halin yanzu dai ana gabatar da wani kwakkwaran bincike akan masu aikin gidan tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan da 'yan uwansa, bayan an nemi gwala-gwalai da kudinsu ya kai kimanin naira miliyan dari uku, wanda suke mallakin tsohon shugaban kasar.

Wata mata da ake zargi da take aiki a gidan shugaban kasar mai suna, Mrs. Jonathan Aridolf Resort, ana zargin ta samo irin mukullin dakin da gwala-gwalan suke ajiye a ciki.

Jaridar The Nation ta bayar da rahoton cewa wacce ake zwrgin ta shiga gidan shugaban kasar dake Otuoke, cikin karamar hukumar Ogbia, ta dauki gwala-gwalan ciki hadda wata sandarshi ta dogarawa.

"Ba bako ne yayi wannan aikin ba. Barawon ya riga ya san gidan nan. Sun yi niyyar ha'inci ne. Daya daga cikinsu mai aikine, wanda ke rike da mukullin dakin da gwala-gwalan ke ajiye a ciki.

"Sauran kuma suna da dangantaka da tsohon shugaban kasar. Na san jami'an 'yan sanda sun kama wasu daga cikinsu. Ba zan iya fadar kudinsu ba, matar tsohon shugaban kasar ce kawai za ta iya fadar kudinsu.

"Sun riga sun bayyana cewa su suka yi, har an samu an karbi kudin daga hannun wasu daga cikinsu," in ji wani wanda lamarin ya faru a gabansa.

Daga baya an bayyana cewa matar tsohon shugaban kasar Patience Jonathan ta shiga rudani akan satar, inda take mamakin yadda aka yi wadanda ake zargin basu saci gwala-gwalan nata ba suka saci na mijinta.

No comments:

Post a Comment