Tuesday, July 23, 2019

Buhari yayi nadin sababbin minitoci 2019

Shugaba Muhammadu Buhari ya fara fitar da sunayen sabbin ministocinsa.
Bakwai daga cikin ministocin mata ne, kashi 16% kenan wanda kasa da kashi 35% ne da masu fafutika ke bukatar gani a cikin gwamnatin.
Mai bai wa shugaban shawara kan harkokin sada zumunta Bashir Ahmad ne ya fara wallafa sunayen a sahafinsa na Twitter a ranar Talata.
Daga cikin sunayen da aka fitar zuwa yanzu akwai tsofafin minsitocinsa akwai kuma sunayen sabbin mutane da a baya ba sa cikin majalisar zartarwar shugaban.
Tuni dai shugaban kasar ya aike sunayen ga majalisar dattijai domin tantancewa.
Sunayen sababbin ministoci a karon farko
1. Sheikh Isa Ali Pantami - Gombe
2. Sanata Godswill Akpabio - Akwa Ibom
3. Alhaji Sabo Nanono - Kano
4. Gbemi Saraki (Kanwar tsohon shugaban majalisar dattawa Bukola Saraki) - Kwara
5. Rauf Aregbesola tsohon gwamnan - Osun
6. George Akume - tsohon gwamnan - Benue
7. Timipre Sylva - tsohon gwamnan - Bayelsa
8. Sadiya Farouk - Zamfara
9. Maryam Katagum - Bauchi
10. Ramatu Tijjani - Kogi
11. Sanata Olorunnibe Mamora - Legas
12. Sunday Dare - Oyo
13. Festus Keyamo - Delta
14. Sharon Ikeazor - Anambra
15. Sanata Tayo Alasoadura - Ondo
16. Pauline Tallen - Filato
17. Mustapha Buba Jedi Agba -
18. Olamilekan Adegbite - Ogun
19. Mohammed Dangyadi - Sokoto
20. Abubakar Aliyu - Yobe
21. Sale Mamman - Taraba
22. Muhammed Mamood - Kaduna
23. Uce Ogar - Abia
24. Emeka Nwajuiba - Imo
25. Akpa Udo
26. Clement Abam
27. Baba Shehuri - Borno
28. Zubair Dada
29. Adeniyi Adebayo - Ekiti
30. Mohammed Abdullahi
31. Osagie Ehenere
32. Bashir Salihi Magashi - Kano
Tsoffin ministocin da suka dawo
1. Babatunde Fashola - Tsohon Ministan Ayyuka da Gidaje
2. Rotimi Amaechi - Tsohon Ministan Sufuri
3. Ogbonnaya Onu - Tsohon Ministan Kimiyya da Fasaha
4. Adamu Adamu - Tsohon Ministan Ilimi
5. Sanata Chris Ngige - Tsohon Ministan Kwadago H
6. Hadi Sirika - Tsohon Karamin Ministan Sufurin Jiragen Sama
7. Zainab Ahmad - Tsohuwar Ministar Kudi
8. Lai Mohammed - Tsohon Ministan Watsa Labarai
9. Musa Bello - Tsohon Minsitan Abuja
10. Abubakar Malami - Tsohon Ministan Shari'a
11. Sulaiman Adamu - Tsohon ministan ruwa
   By DAN GORUBAR RINGIM

No comments:

Post a Comment