Wednesday, July 31, 2019

Tarihin namarudu

 A kasar Iraqi an haka wani kabari inda aka iske gawar Sarki Namarudu da 

matarsa a cikin kabarin

- An ga wasu gwala-gwalai da lu'ulu'u a cikin kabarin wanda aka yi musu kudi 

kimanin dalar Amurka miliyan talatin da biyar

- Sarki Namarudu dai shine sarkin da ba a taba yin Sarki mai arzikinsa ba a tarihi.

An hako gawar Sarki Namarudu a wani yanki dake kasar Iraqi, gawar ta sa da ta matarsa an same su sanye da kaya na gwala-gwalai da lu'ulu'u wanda aka yi musu kudi kimanin dalar Amurka miliyan talatin biyar ($35m), inda kudin ya kai kimanin naira biliyan sha biyu a kudin Najeriya.

Hotuna: An hako gawar Sarki Namarudu da matarsa a kasar Iraqi, an same su sanye da gwala-gwalai na naira biliyan 12
Sarki Namarudu

Sarki Namarudu dai shine Sarkin da yayi zamani da Annabi Ibrahim (AS), tarihi ya nuna cewa akwai lokacin da Namarudu ya sa bayinsa suka gina wani katon rami ya sanya aka kunna wuta mai karfin tsiya a cikin ramin, sannan ya sanya aka jefa Annabi Ibrahim cikin wutar

No comments:

Post a Comment