Harkar samun kudi a yanar gizo na da yawan gaske a wannan lokaci kuma akwai riba, amma fa sai anyi da gaske. Za’a iya yin shafi a wasu dandalin kamar na facebook, amma a tuna cewa duk karin mutanan da kayi a shafin facebook, kana karawa facebook suna, da kuma kudi. Mun amince cewa facebook sunyi nisa, amma kowa zai iya amfani dasu wajan yada dandalinsa na yanar gizo don samun alheri.
Idan aka bude dandalin “build your website” wato “gina naka shafin intanet”, za’a iya saka tallace-tallacen abubuwan saye da sayarwa har wadanda sauran mutane ke tallatawa; tallace-tallace kamar na google adsence, Yahoo, Microsoft da-dai sauransu duk ana iya sakawa.
Hanyar samun kudi ta tallata manhaja, wato “advertisement”:
Wannan hanyar tafi kowace hanya sauki ta fannin samun kudi ta shafin yanar gizo, kuma duk duniya amfi amfani da ita. Idan kana/kina da dandali dayake da abubuwa masu ma’ana (misalin kamar shafin wannan shafin “Bimas computer”) kuma mutane na zuwa dandalin za’a iya sa tallar “adsence” idan akayi rijista da “google adsence”. Abun da kawai ake bukata shine asusun banki da dalar Amurka, wato “domiciliary account” da kuma adireshin meshafi da google din zasu aikoma mutum da check idan ya/ta sami riba. Check din a dalar Amurka yake zuwa, to dolene a tanadi asusun. Zai fidacewa idan mutum ya hada da adireshin “post office” wato P.O.Box wajan adireshin tura sakonni a google.
Idan akasa talla daya, google nabiya a duk sanda wani me ziyartar shafin ka/ki ya danna shafin tallar. Ba wani kudi dayawa ake samuba, amma ana iya samun kudinda suka kai N1.00 har zuwa dun=baunnai masu yawa. Kar a manta, sai ana da shafi mai ma’ana sannan za’a samu mutane su zo dandalin.
Hanyar samun kudi ta hadayyar dandali wato “Affiliate programs”:
A wannan hanyar kuma, zaka sa hanyar hadayya (link) zuwa wasu dandalin kamarsu “Amazon” (wato shafuka na cinikayya da saye da sayarwa) idan akayi rijista da affiliate program dinsu wanda rijistar anayine a shafin nasu. Idan wanda yaje dandalinsu ta dandalinka yayi siyayya, to zasu baka kashin ribar batare da kayi komaiba.
Hanyar samun kudi ta dandalin siye da siyarwa wato “Ecommerce”:
Wannan hanyar tafi dacewa da harkar me shago, ko mai siye da siyarwa. Ma’ana, idan sana’ar mutum itace ya saya ya siyar to wannan hanyar zatafi dacewa da shi/ita. Zaka/zaki bude dandalin ka/ki, a saka hotunan kayan siyarwar da kuma wasu karin bayanai kamar lambar waya inda idan mutun yaga hotunan kayan yana sha’awar siye zai iya siyayyarsa ta dandalin. misali irin wannan dandali shine Jumia.
Idan mutun bashi da halin bude nasa dandalin a yanar gizo, to zai iyam amfani da wanda muke da shi akan wanna dandalin. Jeka sashen Kasuwa/Classified ads
Idan da neman karin bayani akan yadda za’a iya bude dandali a yanar gizo, to a tuntubemu a Bimas computer
Dan Karin bayani, sai ayi comment a nan kasa. Dafatan anyi rijista da mu.
Allah yabamu sa’a gaba daya
Karin bayani.
Atakaice abunda muke fada anan shine: zaka iya bude website dinka, ka saka tallunan google, da wasu companinnikan dan ka samu kudi. Sannan idan kanaso ka jawo mutane zuwa website dinka, zaka iya amfani da da facebook wajan jawo mutanen. Idan mutanen sukazo shafin naka suka danna (click) akan tallar, zaka samu yan chanji duk sanda aka danna tallar. Nan bada dadewaba, zamuyi sharfin yadda zaka iya bude website dinka ta hanya mafi sauki. Mungode
No comments:
Post a Comment