Ambaliya ruwa ta mamaye gonaki fiye da dari uku a garin Safa dake gundumar Sundumina a karamar hukumar Birnin kudu.
Babban Limamin Safa, Malam Ibrahim Safa ya bayyana haka a lokacin taron gangami da kungiyar taimakon kai-da-kai ta GAKAMAZA ta shirya domin tunkarar ambaliyar.
Ya ce asalin ruwan yana zuwa ne ta hanya daya amma yanzu ruwan ya sake bullo
da hanyoyin guda shida wadda ya yi ambaliyar cikin gonakin shinkafa da dawa,
dan haka akwai barazanar abinci a shekara mai zuwa.A nasa jawabin, Mai Unguwar Safa, Malam Usman Bello ya ce sun yi ganuwa guda biyu daga buhuna
da Hakimin Sundumina ya ba su gudummawa amma sai ruwan ya karya ganawar ya kuma nufi gari.
Mai Unguwar Safa ya yi kira ga Majalisar karamar hukumar Birnin kudu local da
gwamnatin jiha su kai musu daukin gaggawa tun kafin ambaliyar ta shig cikingari.
A nasa bangaren, shugaban kungiyar taimakon kai-da-kai ta GAKAMAZA, Malam
.Idi Malam wanda ya yi kira ga jama’ar garin da su ci gaba da kokarin ginawa ruwan ganuwa, ya ce zai sanar da karamar hukumar Birnin kudu halin da ake cik
i domin daukar matakan da suka dace.
No comments:
Post a Comment