
Mabiya mazhabar Shi'a na kungiyar Islamic Movement in Nigeria, IMN sun ce 'yan sanda sun 'kashe' musu mutum shida sannan da dama sun jikkata, a lokacin zanga-zangar neman a saki jagoransu, Sheikh Ibrahim El-zakzaky.
Sun yi zargin cewa 'yan sandan ne suka 'bude' musu wuta yayin zanga-zangar lumana.
Har yanzu dai rundunar 'yan sandan birnin Abuja ba ta ce komai ba.
Sai dai tuni aka datse manyan hanyoyin da ke hada tsakiyar birnin na Abuja da fadar shugaban kasa da majalisar dokoki da kuma yankunan da kotuna suke.
Gidan talbijin na ChannelsTV ya ce an harbi daya daga cikin ma'aikatansu a ciki a lokacin yamutsin.
No comments:
Post a Comment