Wednesday, July 24, 2019

ALI NUHU ZAI ZAMA MINISTAN WASANNNI DA MATASA A MULKIN BUHARI

Dan Gorubar Ringim Hakimin Majiyawa
Ali Nuhu Zai Zama Ministan Matasa Da Wasanni A Gwamnatin Buhari

Rahotannin da ke yaduwa a shafukan sada zumunta na Facebook, Twitter Da Instagram ya bayyana cewa gwamnonin arewa sun nuna goyon bayan su a kan tsayar da fitaccen jarumin nan na Kannywood Ali Nuhu a matsayin Ministan matasa da wasanni

Jarumin dai ya yi kokari kwarai da gaske wajen taya shugaban kasar kamfen a yankin arewacin Najeriya a lokacin yakin neman zabe

Labarin na zuwa ne bayan wata jita-jitan da aka yada ta cewar wasu daga cikin manyan gwamnonin arewa sun nuna goyon bayansu dari bisa dari ga fitaccen dan wasan domin ya zama daya daga cikin Ministocin shugaba Buhari a kasar nan.

Fitaccen jarumin dai ya nuna soyayyarsa matuka ga shugaban kasa Muhammadu Buhari da kuma gwamnatin APC, domin kuwa yana daya daga cikin jiga-jigan wadanda suka yiwa shugaban kasa Muhammadu Buhari da babbar jam’iyyar APC kamfen a yankin arewacin kasar nan.

No comments:

Post a Comment