Showing posts with label Nishadinkowa.Blogspot.com. Show all posts
Showing posts with label Nishadinkowa.Blogspot.com. Show all posts

Wednesday, July 24, 2019

Littafin Ruwan Bagaja

RUWAN BAGAJA
A cikin farkon zamanin Shaihu dan Ziyazzinu an yi wani mutum motsatsa, wanda a ke kira Koje Sarkin labari. Dalilin da ya sa a ke kiransa haka, don haukansa ba na zagin kowa ba ne, ba kuwa na dukan kowa ba ne. Shi dai ba abin da ya ke so sai yaji labari, ya tafi wadansu kasashe, ya rika ba attajirai da sara kuna, su kuwa suna ba shi abinci. In ya ba ka labari, wanda ka ka sani ba, in ka bashi kudi, sai ya debi hamsin ya ba ka. Ya tsare ka, ya ce kai kuma sai ka ba shi wani labari, wanda shi kuma bai sani ba.
Yana cikin bin kasashe, har ran na Allah ya sa ya isa wani gari wai shi kwantagora, wani babban birni ne a cikin kasar Sudan. Ya isa wajen Sarkin garin, aka kai shi masauki. Da ajeyi kayansa, sai ya fito kofar fada, ya shiga halinsa na neman labaru da ba su. Ya kwana kamar uku yana ba sarki labarurruka, fadawa kuwa suna biyansa da wadansu labaru, watau maimakon wandanda ya ba Sarkinsu. Sarkin kasar ana kiransa Sarkin Sudan.
Yana yawo cikin gari, sai ya isa wani katon gida mai benaye da yawa. Ya tambayi barorin da ya tarar zaune ya ce.  Shin gidan wane ne wannan?
Suka ce,  Wane ne duk duniyan nan bai san Alhaji Imam ba?
Koje Sarkin labarai ya ce musu,  Yana fitowa yanzu?
Suka ce,  Wa zai fito da shi yanzu tun azahar ba ta yi ba??
Koje ya share wuri, ya zauna kan azahar ta yi.
Azahar na yi, sai sai suka ji taf, taf; duk zaure aka tashi. Da maigida ya shigo aka fadi aka yi gaisuwa. Da ya zauna ya dubi koje ya ce,  Wannan fa wane ne?
Koje ya ce,  Ni ne Sarkin labari, yau kwanana goma nan garin, ka ji ka ji safarata ka kuwa ji yadda a ke biyana, ko kana iya saye? Maigida ya ce,  To, fadi muji. Yau Allah ya gama ka da gamonka.
Koje ya yi murmushi ya ce,  To, sai dai ma ce Allah ya gama kowa da gamonsa.
Sa an nan fa Koje Sarkin Labari ya tsunke. Ya yi ta zuba labaru, ba ya ko wakafe balle aya.Da ya fadi kamar talatin, sai ya ce wa mai gida,  Biya wadannan tukun, na an nan in ji karfin ci gaba.
Maigida ya ce,  Kara dai! ya yi ta zubawa, har Allah ya gajishe shi. Da ya kare, zuwa magariba, sai maigida ya ce,  To, duk kai labarunka ashe ba su fi a ba da su daga safe zuwa magariba ba, har a ke kiranka Koje Sarkin Labarai ? Kuma ya ce masa,  To, gobe ka zo da kai da abokanka duka, ni kuma in ba ka labarin abubuwan da na yi a duniyan nan, har Allah ya sa na sami arzikin nan da ka gani. Mu gani, in na yi kokari a gajarce labarin, ko ma kare cikin kwana goma ? Koje Sarkin Labari ya duka ya yi ban kwana. Gari na wayewa sai ya taho ya zauna yana jiran maigida. Can zuwa fitowar gana ya fito. Mutanen da ke zaene a zaure suke yi mana barka da kwana. Ya haye kujerarsa ya kame, ya dubi Koje ya ce,  kunnanka nawa?
Koje ya ce,  Biyu,
Ya ce,  To, kara na uku ka sha labari!
Koje ya ce,  To, madalla.I